Sojojin HKI sun kai wasu hare-hare akan sansanin sojan Sanamain dake gundumar Dara’a a kudancin kasar Syria.
Tashar talabijin din da “ Akhbariyyah” ta Syria ta sanar a yau Litinin cewa; sojojin Isra’ila sun kai hari akan sansanin soja na “Sanamain” wanda yake a gundumar Dar’a, kuma an ga jiragen sama na ‘yan mamaya masu yawa suna shawagi a samaniyar yankin.
Wata majiyar ta Syria ta kuma ambaci cewa; sojojin na HKI sun kursa cikin garin Mu’arrah, tare da yin kutse cikin gidaje masu yawa a ciki da gudanar da bincike a cikinsu.
A yankin Kunaidhara ma an ga sojojin na mamaya suna yin kutse, haka nan kuma sun kai hari akan filin saukar jiragen sama na Tpor, da kuma wani filin saukar jiragen sama na soja a Tadammur.
Tun bayan da gwamnatin Basshar Assad ta fadi ne dai HKI ta bude kai wa makamai da cibiyoyin sojan kasar hare-hare babu kakkautawa. A cikin kwanakin farko na faduwar gwamnatin Asad, sojojin HKI sun sanar da cewa sun rusa tsakanin kaso 70% zuwa 80% na jumillar makaman da Syria take da su, na sama, kasa da na ruwa.