Syria: Isra’ila Ta Kai Hari A Kan Sansanin Soja A Yankin Dar’a

Sojojin HKI sun kai wasu hare-hare akan sansanin sojan Sanamain dake gundumar Dara’a a kudancin kasar Syria. Tashar talabijin din da “ Akhbariyyah” ta Syria ta sanar a yau Litinin cewa; sojojin Isra’ila sun kai hari akan sansanin soja na “Sanamain” wanda yake a gundumar Dar’a, kuma an ga jiragen sama na ‘yan mamaya masu […]
Jam’iyyar “Turkish National Party” Ta Tsaid Imam Uglu A Matsayin Dan Takarar Shugaban Kasa

Jami’iyyar adawa ta “Turkish National Party” ta bayyana cewa dan takararta a zaben shugaban kasa na 2028 shi ne magajin garin Istanbul Akram Imam Ugulu wanda a halin yanzu yake a gidan kurkuku. Imam Uglu dan shekara 53 shi ne muhimmin dan takarar shugaban kasa a tsakanin ‘yan hamayya da ake hasashen cewa zai iya […]
Harin Neman Shahada Ya Kashe ‘Dan Share Wuri Zauna Daya A Garin Haifa

Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa; An kai hari nau’i biyu, da ya hada amfani da motar take mutane da kuma bude wuta daga bindiga. Harin da aka kai a kusa da yankin “Yukna’am Iliyat” dake gabashin garin Haifa, ya yi sanadiyyar halakar wani dan share wuri zauna da kuma jikkata wani guda daya. […]
Shugaban Majalisar Dokokin Lebanon Ya Yi Gargadi Akan Masu Tunanin Kulla Alakar Kasar Da HKI

Shugaban majalisar dokokin kasar Lebanon Nabih Barri ya jaddada cewa; HKI tana kokarin jefa Lebanon cikin tarkon kulla alaka da ita, yana mai jaddada cewa; Ko kadan Lebanon ba ta kama wannan hanyar ba. Nabih Barri ya bayyana yadda wasu rahotanni daban-daban suke Magana akan cewa Amurka tana kai gwauro da mari, domin ganin an […]
Arakci: Babu Wanda Zai Yi Tunanin Kawo Wa Iran Hari

Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Iran tana cikin shirin ko-ta-kwana akan duk wani abu da zai iya bijirowa, kuma a halin yanzu ba batun yaki ake yi ba. A wata ganawa da ministan harkokin wajen na Iran ya yi da tawagar kungiyar agaji ta “Red Cross” a karkashin jagorancin shugabanta Koliband, ministan harkokin […]
Iran ta yi gargadin cewa keta hurumin Lebanon da Isra’ila ke yi barazana ne ga zaman lafiyar duniya

Iran ta yi gargadin cewa zaluncin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi wa kasar Labanon na da matukar hadari kuma barazana ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa, inda ta bukaci kasashen duniya da su dauki matakin da ya dace. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei ya yi kakkausar suka kan hare-haren […]
An yi wa Jakadan Afirka ta Kudu da Amurka ta kora tarbar Jamurumai bayan komawarsa gida

Ebrahim Rasool, jakadan Afirka ta Kudu da gwamnatin Trump ta kora, ya samu tarba a wannan Lahadin daga daruruwan magoya bayansa da suke rera wakoki domin karrama shi a filin jirgin sama na Cape Town. Jama’a sun kewaye Rasool da matarsa Rosieda bayan isowarsu, yayin da ‘yan sanda suka yi musu rakiya har zuwa tashar […]
Ana ci gaba da gudanar da zanga-zangar goyon bayan Falastinu a kasashen duniya

Dubban mutane ne a birnin Amman babban birnin kasar Jordan suka gudanar da zanga-zanga bayan sallar Juma’a domin yin Allah wadai da sake dawo da laifukan da Isra’ila ke aikatawa a Gaza. A rahoton factjo, dubban mutane sun bayyana goyon bayansu ga al’ummar Gaza a wani gagarumin maci na wannan Juma’a. Mahalarta tattakin sun yi […]
Duniya na ci gaba da yin tir da Isra’ila kan dawo da hare-harenta a Gaza

Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Turai sun ce, tsagaita bude wuta nan take a Gaza ya zama dole. Da yake magana a wani taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, mataimakin babban sakataren majalisar kan harkokin siyasa Khaled Khari, ya ba da rahoto game da tabarbarewar al’amura a Gaza bayan da Isra’ila ta karya yarjejeniyar […]
UNICEF: Yara a Gaza suna fama da matsalar kwakwalwa da ba a taba ganin irinsa ba

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya sanar da cewa, yara a Gaza suna fuskantar matsakar kwakwalwa da ba a taba ganin irinsa ba a kan kananan yara. “Ba mu da wani bayani a tarihin wannan zamani dangane da ke bukatar tallafin lafiyar kwakwalwa kamar yaran Gaza,” in ji mai magana […]
Iran da Masar sun tattauna kan rikicin da Isra’ila ta jefa yankin gabas ta tsakiya

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya yi kira ga kasashen duniya da su kawo karshen rikicin da Isra’ila ke ci gaba da haifarwa a yankin gabas ta tsakiya. A wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Masar Badr Abdelatty, Araghchi ya yi Allah wadai da sabbin hare-haren da Isra’ila ke kai wa […]
Babban Kusa A Kungiyar Hamas Salah Al-Bardawil Ya Yi Shahada

Kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Hamas ta fitar da wata sanarwa dangane da shahadar Salah al-Bardawil, mamba a ofishin siyasa na kungiyar kuma wakilin majalisar dokokin Falasdinu. A rahoton tashar Al-Alam, bayanin Hamas yana cewa: Dr. Salah Al-Bardawil, wanda ya yi fice a fagen siyasa, kafofin watsa labarai, da fagage na kasa da kasa, kuma ake […]
Syria: SOHR ta fallasa jami’an tsaron sabuwar gwamnati na yi wa tsiraru kisan gilla

Kungiyar da ke sa ido da kare hakkin dan adam ta Syria (SOHR) ta fitar da fayafan bidiyo guda hudu da ke dauke da hotunan azabtarwa da kisa da jami’an tsaron sabuwar gwamnatin kasar karkashin kungiyar Tahrir Sham suke aiwatarwa a kan fararen hula tsiraru marasa rinjaye a kasar. Kungiyar da ke sa ido kan […]