Switzerland: Kama Maduro ya keta kariyar diflomasiyya da dokokin kasa da kasa

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Switzerland ta tabbatar da cewa kamen da Amurka ta yiwa shugaban kasar Venezuela Nicolás Maduro ya zama cin zarafi ga dokokin

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Switzerland ta tabbatar da cewa kamen da Amurka ta yiwa shugaban kasar Venezuela Nicolás Maduro ya zama cin zarafi ga dokokin kasa da kasa da ‘yancin cin gashin kai na Venezuela, da kuma keta kariyar Maduro.

Ma’aikatar ta kuma tabbatar da cewa babu hujjar harin da Amurka ta kai kan Venezuela, tana mai nuna damuwa game da abin da wannan aikin zai iya haifarwa a duniya.

Amurka ta kaddamar da hari a Caracas babban birnin kasar Venezuela, inda ta kai hari a tashoshin jiragen ruwa, filayen jiragen sama, da sansanonin soji. An yi garkuwa da shugaban kasar Venezuela Nicolás Maduro da matarsa tare daukarsu ​​zuwa birnin New York.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted