A hukumance gwamnatin kasar sumaliya ta bukaci HKI ta janye sanarwar da ta fitar na amincewa da yankin sumaliland a matsayin kasa mai yancin kanta, kuma ta bayyana mataki a matsayin haramtacce kuma ya keta alfarma da mutuncin kasarta.
Wadannan kalamai sun fito ne a wata hira da gidan talabijin din Aljazeera dake doha yayi da ministan harkokin wajen kasar sumaliya Ali Omar, inda yayi tir da matakin da gwamnatin sahyuniya ta dauka kuma ta bayyana shi a matsayin zalunci da baza a taba amincewa da shi ba, kuma tsoma baki ne da ya saba ma doka kan harkokin cikin gidan sumaliya,
Yace sumaliya za ta yi amfani da matsin lambar diflomasiya don tunkarar wannan mataki, inda a ranar jumaa da ta gabata ne Isra’Ila ta amince da yankin sumaliland a matsayin kasa mai cin gashin kai a hukumance a wani mataki da ba shi da wani fifiko a matakin kasa da kasa.
Yankin sumaliland ya sanar da samun yancin kai daga kasar sumaliya a shekara ta 1991 sai dai matakin bai samu amincewa ba daga wani mamba a majalisar dinkin duniya ba.