Kasashen Larabawa Sun Gudanar Da Taron Gaggawa Kan Rikicin Somalia Da HKI

Kwamitin tsaro na MDD da kuma kungiyar kasashen Larabawa zasu gudanar da tarurruka daban daban a yau da kuma cikin wannan makon don tattauna batun yankin Somaliland wanda yake son ballewa daga kasar Somalia, wanda kuma HKI ta amince da ballewarsa a hukumance. Tashar talabijan ta Press Tv a nan Tehran ta bayyana cewa a […]
Sheikh Qaseem: Kwance Damarar Hizbullah, Shiri Ne Na Amurka Da HKI

Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’eem Qaseem ya bayyana cewa shirin kwance damarar mayakan kungiyarsa shiri ne na HKI da Amurka, ko da sun kira shi takaita makamai hannun gwamnati, kuma Lebanon ba zata taba fita cikin matsalolin da take ciki ba matukar HKI bata aiwatar da shirin tsagaita wuta da aka cimma […]
Iran Ta Harba Taurarin ‘Yan’adam Guda 3 Zuwa Sararin Samaniya A Rasha

JMI ta cilla taurarin ‘yan’adam guda uku a lokaci guda tare da amfani da kumbon kasar Rasha mai suna Yoyuz a dazo da misalin karfe 4.48 na yamma agogon Tehran. Jami’an gwamnatin kasar Iran sun bayyana cewa sun cilla wadan nan taurari 3 ne a ciyar cilla taurarin ‘yan’adam na kasar Rasha mai suna Vostochny […]
Hemomin ‘Yan Gudun Hijiran Falasdinawa A Gaza Sun Fada Cikin Ambaliyar Ruwa

A dai dai lokacinda HKI take ci gaba da hana shigowar kayakin agaji cikin zirin gaza, wanda ya sabawa yarjeniyar tsagaita budewa juna wuta da suka cimma a cikin watan Octoban da ya gabata, ambaliyar ruwa ta shiga dukkan tentuna falasdinawa yan gudun hijira a yankin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto […]
Iran Da Qatar Suna Goyon Bayan Mutanen Yemen A Rikici Kudancin kasar

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi da tokwaransa na kasar Qatar kuma firay ministan kasar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman bin Jassim Al Thani sun bukaci kasashen UAE da kuma Saudiyya sun mutunta ‘yancin kasar Yemen da hadin kan kasar a rikicin da kasashen biyu suke yi a kudancin Yemen. Tashar talabijan ta Presstv a […]
Isra’ila, Amurka, da Turai na yaki da Iran_Pezeshkian

Shugaban kasar Iran Massoud Pezeshkian, ya bayyana cewa a halin yanzu Isra’ila, Amurka dama Kasashen Turai na yaki da Iran. Mista Pezeshkian ya bayyana hakan ne a wata hira da a wata hira ta musamman da kafar yanar gizo ta ofishin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci. Ya ce yayin da Amurka, Turai, da Isra’ila ke […]
Kwamitin Tsaro na MDD zai yi zaman gaggawa game da amincewar Isra’ila da Somaliland

Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai kira wani zaman gaggawa a ranar Litinin, biyo bayan da Isra’ila ta amince da yankin Somaliland a matsayin kasa mai cin gashin kanta. Kwamitin Tsaron zai yi zaman ne bayan da Isra’ila ta amince da Somaliland, jamhuriya mai ikirarin cin gashin kanta wadda ta balle daga Somaliya. A […]
Kashi 63% na Amurkawa ba su gamsu da tsarin tattalin arziki na Trump Ba

Wani binciken da kungiyar YouGov ta gudanar ya nuna cewa kashi 63% na Amurkawa basu gamsu da tsarin tafitar da tattalin arziki na shugaban kasar Donald Trump ba. Ra’ayin Amurkawa game da yadda Shugaba Donald Trump ke tafiyar da tattalin arziki ya tabarbare a wannan shekarar, bisa ga sabon binciken YouGov da aka gudanar wa […]
Guinea : Ana Zaben shugaban kasa mai manufar maida kasar bisa tsarin mulki

Yau Lahadi al’ummar Guinea ke kada kuri’a a zaben shugaban kasar mai manufar mayar da kasar bisa tsarin mulki shekaru hudu tun bayan da sojoji suka kifar da mulkin Alpha Conde. Kimanin ‘yan kasar miliyan 6.7 da suka cacanci zabe ke kada kuri’a a zagaye na farko na zaben shugaban kasar. ‘Yan takara takwas […]
Putin ya yi barazanar warware rikicin Ukraine da karfin soja_Putin

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi barazanar warware rikicin Ukraine da karfin soja muddin Kyiv ta ki karbar hanyar lumana. Idan Kyiv ba ta son warware rikicin cikin lumana ba, Rasha za ta warware shi da karfi inji Putin. Ya sake nanata cewa Moscow za ta cimma dukkan manufofin aikin soja na musamman, ko dai […]
AFCON : Najeriya Ta Tsallaka Zuwa Mataki Na Gaba

Tawagar kwallon kafa ta Najeriya da ke buga gasar kofin kasashen nahiyar Afirika yanzu haka a kasar Morocco ta samu nasarar kai wa matakin zagayen ‘yan 16 bayan ta doke kasar Tunisia a wasa na biyu da ta buga a rukunin C na gasar. Nijeriya ta zama kasa ta biyu bayan Masar da ta samu […]
Sumaliya Ta Bukaci Isra’ila Ta Janye Sanarwar Amincewa Da Yankin Sumaliland

A hukumance gwamnatin kasar sumaliya ta bukaci HKI ta janye sanarwar da ta fitar na amincewa da yankin sumaliland a matsayin kasa mai yancin kanta, kuma ta bayyana mataki a matsayin haramtacce kuma ya keta alfarma da mutuncin kasarta. Wadannan kalamai sun fito ne a wata hira da gidan talabijin din Aljazeera dake doha yayi […]
Jakadan Iran A Iraki: Amurka Na Amfani Da Sararin Samaniyar Iraki Don Leken Asiri A Kasar Iran

Jakadan kasar iran a birnin Bagadaza na kasar Iraki Mohammad Kazem Ale sadeq ya bayyana cewa jamhuriyar musulunci ta iran ta gano cewa jiragen leken Asirin Amurka suna amfani da sararin samaniyar iraki don leken Asiri a kasar Iran. Jakadan yayi wannan bayanin ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a jiya Asabar […]
Masu zanga-zanga A birnin London Sun Bukaci A Saki Daraktan Asibitin Gaza

Masu rajin kare hakkin falsdinawa sun gudanar da zanga-zanga a birnin London na birtaniya, kuma ta farko a irinta ta tunawa da zagayowar ranar da sojojin Isra’ila suka kama Dr Hussam Abu safiya Daraktan Asibitin Kama lAdwan dake kudancin gaza , kuma sun yi kira da a gaggauta sakinsa bayan kwashe shakara daya a tsare. […]