Sumaliya Ba za Ta Taba Bari Isra’ila Ta Kasance A Kasarsu Ba

shugaban kasar sumaliya yace bazai taba bari ba ko ta wanne hali isra'ila ta kasance acikin kasarta

Shugaban kasar sumaliya hassan shaikh mahamud ya bayyana cewa kasahen dake kahon Afrika ba za su taba bari HKi ta kasance a kasashensu ba karkashin kowanne irin yanayi, kuma ya fadi hakan ne a tattaunawa da gidan talabijin din Aljazeera ta yi da shi,  ya kara da cewa gwamnatin mamaya ta telaviv tana shirin kafa sansaninta na sojin ruwa a tashar ruwa ta Berbera dake tekun Adan a Somaliland, wani yanki da ya bayyana kansa a matsayin jamhuriyar arewa maso yammacin somaliya

Shugaban na Somaliya ya kara da cewa babban burin isra’ila shi ne ta kara samun kusanci da kasahen larabawa dake gabar tekun parisa da kuma kasar Iran, da kuma tsarin da take kokarin aiwatarwa da ta kira shi a matsayin babbar isra’ila.

kalmar isra’ila mai fadi an sake dawo da ita a cikin tattaunawar siyasar isra’ila ne a yan shekarun nan, a watan Agustan shekarar da ta gabata inda fira ministan isra’ila benyamin natanyaho ya shaidawa kafofin yada labaran isra’ila cewa yana jin kusanci sosai da wannan hangen nesa, wanda ake nufi da yankunan falasdinawa da isra’ila ke mamayewa tare da wasu sassan kasashen masar, jodan, siriya, da labanon  kuma ya bayyana hakan a matsayin aiki mai muhimmanci na tarihi da kuma na ruhaniya

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted