Sudan: Sojoji na ci gaba karbe mahimman gine-gine a birnin Khartoum

A Sudan bayan sake karbe fadar shugaban kasa da ke birnin Khartoum, sojojin kasar sun ci gaba da kai farmaki a babban birnin kasar a

A Sudan bayan sake karbe fadar shugaban kasa da ke birnin Khartoum, sojojin kasar sun ci gaba da kai farmaki a babban birnin kasar a ranar Asabar, inda suka sake karbe iko da wasu gine-gine, ciki har da babban bankin kasa da hedkwatar hukumar leken asiri da kuma gidan adana kayan tarihi na kasar.

Ana kallon wannan a matsayin nasarorin ga Janar al-Burhan a babban birnin kasar, wanda rikicin cikin gida ya rutsa da shi na tsawon shekaru biyu.

A wannan Asabar, kakakin rundunar sojojin kasar, Janar Nabil Abdullah, ya sanar a cikin wata sanarwa cewa sojojin na ci gaba da samun nasara a birnin Khartoum, Ya kuma ce sojojin sun “kore daruruwan ‘yan bindiga.

A sa’i daya kuma, ana ci gaba da gwabza fada a yankin Darfur, wanda kusan yana karkashin ikon dakarun RSF.

A cewar masu fafutukar kare hakkin jama’a, akalla fararen hula 45 ne aka kashe a ranar Alhamis a wani harin da dakarun sa kai suka kai a garin Al-Malha da ke arewacin Darfur.

Sojojin sun yi ikirarin cewa sun yi wa garin kawanya tare da kashe makiya sama da 380.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments