Gwamnatin yankin Kurdufan ta Arewa ta sanar da cewa; rundunar kai daukin gaggawa ta “RSF” ta kai hare-hare da jirage marasa matuki akan gidaje da cibiyoyin farafen hula a cikin garin al-baidh da har zuwa yanzu ba a tantance adadin wadanda lamarin ya rutsa da su ba.
Hukumar yankin ta yi tir da harin a wani bayani da ta fitar sannan kuma ta zargi kungiyar da cewa, ba ta kimanta ko ganin hurumin fararen hula da dukiyoyinsu.
Hukumar ta kuma yi kira ga ‘yan kasa da su kasance a cikin fadaka da kuma aiki da bayanan da suke fitowa daga hukuma akan matakan da ya kamata su rika dauki a yanayi irin wannan.
Wannan dai ba shi ne karon farko da mayakan rundunar kai daukin gaggawar ta kai hari a cikin garin na al-baiydh ba, domin a ranar 1 ga watan Oktoba ta kashe mutane hudu a harin da ta kai wa tsangayar daliban jami’a a Kurdufan, da kuma jikkata wasu mutane 47.
Gwamnatin kasar Sudan da kuma kungiyoyin kare hakkin bil’adama suna zargin dakarun kai daukin gaggawa da kai hare-hare akan cibiyoyin fararen hula.