Sudan: Mutane Da Dama Sun Jikkata Sanadiyyar Harin RSF A Kudancin Kurdufan

Majiyar sojan Sudan ta ce, harin da dakarun “RSF” ne su ka kai da jiragen sama marasa matuki akan cibiyar ‘hukumar leken asiri” a garin

Majiyar sojan Sudan ta ce, harin da dakarun “RSF” ne su ka kai da jiragen sama marasa matuki akan cibiyar ‘hukumar leken asiri” a garin Kaduqli, ya yi sanadin mutuwar mutane da kuma jikkatar wasu.

Bugu da kari, rundunar ta kai wani harin aka wata motar farar hula da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 4 da kuma jikkatar wani guda daya.

 A wani labarin daga sudan MDD ta fitar da wani rahoto akan yadda aka ci zarafin mata da ‘yan mata tare da cewa; “Munin Lamarin ya fi karfin a iya kwantanta shi.”

 Jami’a mai shiryawa MDD rahoto akan cin zarafin mata, Rim as-Salim ya kuma ambaci labari masu firgitarwa akan yadda mayakan na rundunar kai dauki gaggawa “RSF” suka mayar da cin zarafin mata wani salon yaki domin rusa al’ummar Sudan.

Rahoton ya ambaci jahohin Jazira, khartum, Bahral-Ahmar, da kuma Shumaliyyah, a matsayin wuraren da aka ci zarafin matan.

Al-salim ta kuma ce, abinda ya rika faruwa ba wai aiki ne na daidaikun mutane ne, wani tsari ne da mayakan suke amfani da shi domin rusa al’ummar sudan.

Wani sashen na rahoton ya ambaci yadda mayakan suke kwace da raba mutane da dukiyar da suke da ita, ta hanyar kai wa gidajensu hare-hare da kwace gwala-gwalai da duk wani abu mai kima.

Haka nan kuma ta yi suka akan yadda duniya ta gajiya wajen bayar da taimako da agaji ga mutanen na Sudan, wanda ta ce ya zuwa yanzu abinda ake bayarwa bai  kai  kaso 38% na abinda ake da bukatuwa da shi ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted