Iran : Shugaba Pezeshkian ya taya Kiristoci murna

Shugaban kasar Iran Massoud Pezeshkian ya aike da sakon taya murna ga kiristocin duniya a dalilin bikin Kirsmeti da mabiya addinin kirista ke bikin zagayowar ranar haihuwar Yesu Almasihu. Mista Pezeshkian ya aike da sakon murnar bikin tare da na Sabuwar Shekara ga shugaban Cocin Katolika Paparoma Leo XIV. A a sakon da ya aike, […]
Kyaftin Traoré na Burkina, ya karbi shugabancin AES

Shugaban kasar Burkina faso, Kyaftin Ibrahim Traoré ya karbi shugabancin karba karba na kungiyar hadakar kasashen sahel ta AES. Ya karbi shugabancin ne daga hannun takwarsansa na Mali Janar Asimi Goita, bayan taron koli na shugabancin kungiyar. Sabon shugaban kungiyar AES ya tabbatar da jajircewa wajen ci gaba da habaka kungiyar. Ya sake jaddada manufofinsu […]
Aljeriya Ta ayyana mulkin mallakar Faransa a matsayin babban Laifi

Majalisar Dokokin Aljeriya ta amince da wata doka da ta ayyana mulkin mallaka na kasar Faransa a matsayin babban laifi tare kuma da bukatar Faransar ta nemi afuwar kasar a hukumance. Matakin dai na zuwa ne a daidai lokacin da dangantakar difflomatsiyya tsakanin Algers da Paris ke kara tsami. Daftarin dokar dai na daga cikin […]
Isra’ila na ci gaba kai Hare-hare Kan Gaza

Isra’ila ta ƙaddamar da sabbin hare-hare ta sama da manyan bindigogi a Gaza, wanda ke nuna yadda take ci gaba da karya yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma toshe hanyoyin agajin jin kai da yankin Falasdinawa ke matukar bukata. Kafafen yada labarai na Falasdinawa sun ruwaito cewa Isra’ila ta yi ruwan bama-bamai a gefen gabashin birnin […]
AFCON: Burkina ta doke Equatorial Guinea 2-1, Aljeriya ta lallasa Sudan 3-0

A ci gaba da gasar cin kofin kwallon kafa na Afrika da yanzu haka ke gudana a Morocco, Burkina Faso ta doke Equatorila Guinea 2-1, yayin da Aljeriya ta lallasa Sudan da 3-0 a wasansu na ranar Laraba. Haka zalika a ranar ta Laraba Ivory Coast ta doke Mozambique da 1-0 Sai kuma Kamaru wacce […]
Sudan: Mutane Da Dama Sun Jikkata Sanadiyyar Harin RSF A Kudancin Kurdufan

Majiyar sojan Sudan ta ce, harin da dakarun “RSF” ne su ka kai da jiragen sama marasa matuki akan cibiyar ‘hukumar leken asiri” a garin Kaduqli, ya yi sanadin mutuwar mutane da kuma jikkatar wasu. Bugu da kari, rundunar ta kai wani harin aka wata motar farar hula da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 4 […]
Lebanon: Sojojin “Isra’ila” Ta Kai Hare-hare A Yankin Bika

Mutane da dama sun jikkata sanadiyyar wani hari da jirgin sama maras matuki na “Isra’ila” ya kai akan wata mota a garin Hush sayyid Ali dake Bika a gabashin kasar ta Lebanon. Bugu da kari a lokaci daya Haramtacciyar kasar Isra’ila ta kuma kai wasu hare-hare a kudancin Lebanon a yau Alhamis, wanda ci gaba […]
Korea Ta Arewa Ta Yi Gwajin Sabon Makami Mai Linzami Dake Cin Dogon Zango

Kafafen watsa labarun kasar Korea Ta Arewa sun bayar da labarin cewa, shugaban kasar Kim Jung Un ya halarci inda aka yi gwajin makami mai linzami mai cin dogon zango da aka harba a kusa da gabar ruwan ta gabas. Kamfanin dillancin labarun kasar ta Korea Ta Arewa ya ce, an yi gwajin ne a […]
Fira Ministan Iraki Ya Yi Watsi Da Kiran Wani Malamin Addinin Kiristan Na Kulla Alaka Da “Isra’ila”

Fira ministan Iraki Muhammad Shi’ya Sudani ya mayar da martani akan wani malamin addinin kirista na kasar ya yi akan a kulla hulda da Haramtacciyar Kasar Isra’ila. Shugaban majami’ar Kildanawa Louise Rufael Sako wanda ya gabatar da jawabi na kirsimeti a gaban fitattan ‘yan siyasa da malaman addini na Iraki ya yi kira zuwa kulla […]
Sudan: Mutane Da Dama Sun Jikkata Sanadiyyar Harin RSF A Kudancin Kurdufan

Majiyar sojan Sudan ta ce, harin da dakarun “RSF” su ka kai da jiragen sama marasa matuki akan cibiyar ‘hukumar leken asiri” a garin Kaduqli, ya yi sanadin mutumar mutane da kuma jikkatar wasu. Bugu da kari, rundunar ta kai wani harin aka wata motar farar hula da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 4 da […]
Aragchi Ga Amurka: Diblomasiyya Ba Dai Dai Yake Da Bude Wuta Ba

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa diblomasiyya ba shi ne aika boma bomai ba, kamar yadda gwamnatin Amurka take son mu fahinta. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalyo Jakadan kasar Amurka a MDD Morgan Ortagus yana fada a wani taron kwamitin Tsoro na majalisar a farkon wannan makon, […]
Iran Ta Kwace Jirgin Ruwa Dauke Da Man Fetur Lita Miliyan 4 Na Sata

Majiyar dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran wato IRAGC ta bada labarin cewa sun kwace wani jirnin ruwa na kasashen waje dauke da man fetur kimani lita miliyon 4 yana kokarin ficea daga kasar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto majiyar tana cewa, kasar Iran tana fama da […]
Yansanda A HKI Sun Yi Sun Kama Masu Bukukuwan Kirsimeti A Birnin Haifa

Majiyar labarai daga birnin Haifa da aka mamaye ya nuna cewa yansanda a haramtacciyar kasar ta hana kiristoci gudanar da bukukuwan kirsimeti a unguwar Wadi-Al-Nisnas na birnin Haifa, saboda aiwatar da dokar da HKI ta kafa na takaita ayyukan sauran addinai a kasar in banda addinin yahudawa, Kamfanin dillancinlabarai IP na kasar Iran ya nakalto […]
Zelesky Ya Ce A Shirye Yaki A Samarda Yankin Da Ba Aikin Soje A Tsakanin Rasha Da Ukraine

Shugaban kasar Ukrain Volodimir Zelesky ya bayyana cewa a shirye yake ya janye sojojinsa daga gabacin kasar Ukraine sannan idan kasar Rasha ma ta amince zasu samar da yankin da babu yaki a tsakanin kasashen biyu idan ana son kawo karshen yakin da ke faruwa a yankin Dambas. Ya ce idan haka ya faru sojojin […]
NLC Ta Bukaci Yan Najeriya Sun Ki Amincewa Da Dokar Sabon Haraji

Shugaban kungiyar kwadago a tarayyar Najeriya yayi kira ga mutanen kasar su ki amince da dokokin haraje wadanda babu adalci a cikinsu. Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta nakalto shugaba NCL Joe Ajaero yana fadar haka a jawabinsa na karshen shekara ga yan Najeriya ya kuma kara da cewa a wannan lokaci kuma nan gaba […]