Spain Ta Aike Da Jirgin Ruwan Don Taimakawa Tawagar Flotilla Zuwa Gaza.

Prime ministan  kasar spain pedro Sanches ya fitar da wannan sanarwar ne a birnin new York inda ya bayyana cewa za’a aike da jirgin ruwa

Prime ministan  kasar spain pedro Sanches ya fitar da wannan sanarwar ne a birnin new York inda ya bayyana cewa za’a aike da jirgin ruwa na soji mai dauke da kayan aiki na bada kariya daga Cartagena ,don daukar mataki  ko da bukatar Haka ta taso na taimakawa  tawagar agaji na Flotilla da ke kan hanyar zuwa Gaza dauke da kayan Agaji domin bada taimakon gaggawa ga yankin falasdinu.

Wadanda ke kula da tawagar ta Flotilla sun bada rahoton cewa abubuwan 12 ne suka fashe a lokaci da aka kaiwa jiragen ruwa guda 9 hari acikin ruwan kasa da kasa, sai dai yazuwa yanzu Isra’ila da take ta yi musu barazana na hana tawagar zuwa ko ina ta yi shiru .

Wannan yana zuwa ne adaidai lokacin da majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa Isra’ila tana kisan kare dangi a gaza  inda sama da mutane 65000 suka rasa rayukansu tun da ta fara kai hari a watan oktoban  shekara ta 2023, karkashin goyon bayan Amurka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted