Spain : Akalla Mutum 68 Suka Mutu A Hatsarin jirgin Kasa

Hukumomin kasar sun sanar da ayyana zaman makoki na kwana Uku bayan mummunan hatsarin.

Rahotanni daga Spain na nuni da cewa mutane akalla 68 ne suka mutu a hatsarin jirgin kasa a Spain a yayin da kuma aka kiyasta kusan wasu 100 da suka ji rauni.

Tuni hukumomin kasar suka sanar da ayyana zaman makoki na kwana Uku a fadin kasar bayan mummunan hatsarin.

Bayanai sun ce Jiragen kasa biyu ne sukayi karo da juna a ranar Laraba, a kimanin kilomita 150 daga kudancin birnin Madrid.

Firaministan kasar Pedro Sánchez ya nuna kaduwarsa game da hatsarin, yayin da gwamnati da hukumomin yankin, da kuma kungiyoyin agajin gaggawa ke fargabar cewa adadin zai iya karuwa a cikin sa’o’i masu zuwa.

A cewar mai magana da yawun hukumar agajin gaggawa ta Spain da AFP ya tuntuba, ya ce hatsarin ya faru ne da misalign karfe 8:54 na safe a jiya tsakanin jiragen ƙasa guda biyu, daya na kamfanin Yrio mai zaman kansa dayan kuma na kamfanin kasa na Renfe.

Wannan dai shi ne hatsarin jirgin kasa na biyu mafi muni da ya auku a wannan kasar ta Spain a cikin shekara daya.

Ko a watan janairu Andalusia wani hatsarin jirgin kasa na Adamuz ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 40.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted