Somaliya Za Ta Sayi Jiragen Yaki Daga Kasar Pakitsan

Kafafen watsa labarun Turkiya sun ambaci cewa an cimma yarjejeniya a tsakanin kasashen Somaliya da Pakistan akan sayen jiragen yaki 24 samfurin jf-17 thunder, ba
jirgin jf-thunder

Kafafen watsa labarun Turkiya sun ambaci cewa an cimma yarjejeniya a tsakanin kasashen Somaliya da Pakistan akan sayen jiragen yaki 24 samfurin jf-17 thunder, ba tare da an tsaida lokacin karbarsu ba.

Kakafen watsa labarun su ka ce; gwamnatin tarayyar Somaliya ta cimma matsaya da Pakistan akan sayen jiragen yakin da ake kerawa ta hanyar hadin gwiwa a tsakanin kamfanonin Pakitsan da China.

Cinikin jiragen  yakin dai yana a karkashin kokarin da kasar Somaliya take yi ne na sake farfado da sojojinta na sama.

Kafar watsa labarun Turkiya ta “TRHaber” wacce ta dauki labarin ba ta ambaci kimar jiragen ba,kuma babu wata kafa a hukumance ta gwamnatocin kasashen biyu da ta yi Magana akai.

Kamfanonin kasashen Pakistan da China ne dai suke kera jiragen yakin da suke aiwatar da ayyuka mabanbanta a yayin kai farmaki a doron kasa.

A cikin watan Disamba da ya wuce ne dai wata tawaga ta sojan Pakitsan ta kai ziyarar aiki zuwa kasar Somaliya a karkashin jagoranci Air Marshal Muhammad Sarafraz. A yayin ziyarar tawagar sojojin na Pakistan ta gana da shugaban kasar Somaliya Hassan Sheikh Mahmud da Fira minister Hamzah Abdi Berry, da ministan tsaro Ahmad Mu’allim Faqih.

Daga cikin batutuwan da aka tattauna da akwai na bai wa sojojin saman Somaliya horo da su ka hada kanana da manyan jami’ai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted