Kasashen Somaliya da Saudiyya sun sanya hannu kan yarjejeniyar hadin guiwa ta tsakanin sojoji.
Sabuwar yarjejeniyar na da manufar karfafa dangantakar dabaru yayin da Mogadishu ke neman karfafa karfin tsaronta.
Ma’aikatar Tsaro ta Somaliya ta sanar a ranar Litinin cewa Somaliya da Saudiyya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa ta tsaro da soja.
Ma’aikatar ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa yarjejeniyar za ta karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.
Ministan Tsaron Somaliya Ahmed Moallim Fiqi da takwaransa na Saudiyya, Yarima Khalid bin Salman ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar a babban birnin Saudiyya, Riyadh.
Wannan hadin gwiwa na da nufin inganta zaman lafiya da tsaro a yankin a Tekun yankin, a cewar kafofin watsa labarai na Somaliya.
Somaliya dai na neman kulla dangantaka musamman a fannin tsaro tun bayan da Isra’ila ta amince da yankin Somaliland a matsayin kasa mai cin gashin kan ta.