Sojojin Yemen Suna Kara Kama Yankuna A Gundumar Ta’iz

A gefe daya a jiya juma'a ne dai Saudiyya ta kai wasu jerin hare-hare a gundumomin kasar ta Yemen da su ka hada San'aa da
Ansarullah

Tashar talabijin din “almayadeen” ta nakalto majiyar sojojin Yemen suna sanar da samun ci gaba a gundumar Ta’iz, haka nan kuma a gabashi da kudancinta.

Wannan ci gaban na sojojin Yemen yana tafiya kafada-kafada da wasu hare-haren akan sojojin Saudiyya da suke a cikin kasar ta Yemen da suke taimakawa ‘yan korensu.

A gefe daya a jiya juma’a ne dai  Saudiyya ta kai wasu jerin hare-hare a   gundumomin kasar ta Yemen da su ka hada San’aa da Sa’adah ta “Ta’iz.

 Gwamnatin Sanaa tana yin kira ga Saudiyya ne da ta dauke mata takunkumin da ta kakaba mata na ruwa da sama, idan kuma ba haka ba za ta ci gaba da yaki har zuwa lokacin da za ta tilasta mata yin hakan.

Faransa ta aike da sojoji zuwa kasar ta Saudiyya domin taimaka mata a yakin da take yi da kasar Yemen.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted