Kakakin sojojin Yemen Janar Yahya Sari ne ya sanar a jiya Laraba da marece cewa; sojojin kasar sun kai wa hare-hare biyu da jiragen sama marasa matuki zuwa yankunan Yafa da Asqalan dake HKI.
Janar Sari ya ce harin farkon dai sun kai shi ne akan wata cibiya mai muhimmanci a Yafa dake tsakiyar HKI,yayin da hari na biyu su kai kai shi a wani yanki na masana’antu dake Asqalan a kusa da Gaza.
Janar Sari, ya ce sun kai harin ne domin taimakawa Falasdinawa da ake zalunta, kuma harin mataki ne na biyar a jerin hare-haren da suke kai wa HKI.
Kakakin na sojan Yemen ya kuma kara da cewa; Za su cigaba da kai wa HKI hare-haren har sai an kawo karshen yakin Gaza da kuma dauke wa yankin takunkumi.
Kusan kwanaki 4 kenan a jere da sojojin na Yemen suke kai hare-hare da jirage marasa matuki da kuma makamai masu linzami akan muhimman cibiyoyin HKI.