Sojojin Yemen sun Kai Wa HKI Hare-hare Sau 13 A Cikin Kwanaki 10

Kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ta sanar da cewa a cikin kwanaki 10 kadai ta kai wa HKI hare-hare har sau 13. Kamfanin dillancin labarun

Kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ta sanar da cewa a cikin kwanaki 10 kadai ta kai wa HKI hare-hare har sau 13.

Kamfanin dillancin labarun “IRNA” na Iran ya ambato majiyar ta Ansarullah tana cewa, wadannan hare-haren suna  cikin jerin hare-haren taimakawa Falasdinawa ne.

Kakakin sojan Yemen Janar Yahya Sari ya fada wa kafafen watsa labarun kasar cewa mafi yawancin wadannan hare-haren dai sun kai su ne akan birnin Tel Aviv. Haka nan kuma sansanin sojan sama na “Navatim” dake yankin Naqab.

Sojojin na Yemen sun rika yin amfani da makamai masu linzami samfurin “Ballistic’ da su  ka bai wa sunan “Falasdinu 2”,wanda makami ne da ya fi sauti sauri.

A ranar Lahadin da ta gabata ma dai sojojin na kasar Yemen sun harba makami mai linzami akan filin saukar jiragen sama na Ben Gurion dake kusa da Tel Aviv da hakan ya jawo dakatar da tashi da saukar jiragen sama.

Sojojin na Yemen sun ce, sun kai wancan harin ne a matsayin mayar da martani ga harin da HKI ta kai wa biranen Sanaa da kuma Hudaidah.

Har ila yau sojojin na Yemen sun ce za su fadada hare-harensu gwgargwardon yadda sojojin HKI za su kai fadada nasu kai hare-haren.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments