Sojojin Yemen Sun Kai Munanan Hare-Hare Kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Sojojin Yemen sun kai hare-hare kan haramtacciyar kasar Isra’ila ciki har da filin jirgin sama na Ben Gurion da wani jirgin ruwan Amurka da tashar

Sojojin Yemen sun kai hare-hare kan haramtacciyar kasar Isra’ila ciki har da filin jirgin sama na Ben Gurion da wani jirgin ruwan Amurka da tashar wutar lantarki a kudancin Qudus

Sojojin Yemen sun sanar da kai wasu munanan hare-hare guda uku kan haramtacciyar kasar Isra’ila da uwar gijiyarta Amurka da suka hada da babban filin jirgin sama na Ben Gurion da ke yankin Jaffa da tashar wutar lantarki da ke kudancin birnin Qudus da kuma jirgin ruwan Amurka mai dakon jiragen saman yaki na USS Harry Truman a lokacin da suke shirin kai wani gagarumin hari ta sama kan kasar Yemen.

A cikin wata sanarwa da rundunar sojin Yemen ta fitar ta bayyana cewa: Sojojin kasar masu kula da makamai masu linzami sun gudanar da ayyukan soji masu inganci guda biyu, na farko a kan babban filin jirgin saman Ben Gurion na haramtacciyar kasar Isra’ila da ke yankin Jaffa da aka mamaye da makami mai linzami kirar Falasdinu 2.

Yayin da sauran farmakin suka kai kan tashar wutar lantarki a kudancin birnin Qudus da aka mamaye da makami mai linzami nau’in Zul-Fiqar. Kamar yadda sanarwar ta tabbatar da cewa: Makamai masu linzamin biyu sun yi nasarar isa inda aka harba su.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments