Sojojin Yemen sun kai harin makami mai linzami kan yankin da ke kewaye da birnin Qudus da aka mamaye bayan da na’urar kakkabo makamai ya kasa kakkabo shi
Rundunar sojin mamayar Isra’ila ta sanar da cewa: Jami’an tsaron sararin samaniyyar haramtacciyar kasar Isra’ila sun gano wani makami mai linzami da aka harba daga kasar Yemen, da ya fada a matsugunin Modi’in da ke kewaye da birnin Qudus.
Rahotonni sun bayyana cewa: An yi ta jin karar kararrawar gargadi a yankunan da suke tsakiyar Falasdinu da aka mamaye bayan da aka gano harba makami mai linzami daga Yemen, kuma jami’an tsaron cikin gidan haramtacciyar kasar Isra’ila sun bayyana cewa: An yi ta jin karar gargadi a cikin matsugunan yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida da birane sama da 150 a cikin sa’o’in wayewar garin yau Juma’a, amma ba a yi nasarar kakkabo makamin ba har sai da ya kai inda aka tsaita shi.
Mahukuntan haramtacciyar kasar Isra’ila ba su bayyana irin barnar da makami mai linzamin ya janyo ba, amma sun yi furuci da rashin iya kakkabo shi.