Sojojin Yemen sun kai hari kan wani sansanin sojin haramtaciyar kasar Isra’ila da makami mai linzami
Kakakin Rundunar Sojin Yemen Birgediya Janar Yahya Sari’e ya sanar da cewa: Sojojin Yemen sun kai hari da makami mai linzami kirar “Falasdinawa 2” kan wani sansanin sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da ke yankin Jaffa da aka mamaye.
Birgediya Janar Sari’e ya kara da cewa: Wannan farmakin ya zo ne a cikin tsarin mataki na biyar na ci gaba da goyon bayan al’ummar Falastinu da ake zalunta da kuma mayar da martani ga kisan gillar da ake yi musu.
Sanarwar da Rundunar Sojin Yemen ta fitar ta kara da cewa: Sojojin Yemen suna ci gaba da kai hare-haren soji kan makiya yahudawan sahayoniyya ne a yankunan da suka mamaye na Falasdinawa.
Sojojin Yemen dai sun jaddada cewa: Gwagwarmayarsu ba zata tsaya ba, har sai an kawo karshen kai hare-haren wuce gona da irikan Gaza, sannan kuma aka dage matakin killace yankin, kakakin sojin ya mai cewa: Suna tabbatar da cewa, tare da ‘yan gwagwarmayar al’ummar Yemen suna shirye su tunkari duk wani wuce gona da iri na haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka da dukkanin karfinsu.