Sojojin Yemen Sun Kai Hari Da Makami Mai Linzami Akan HKI

A wata sanarwa da kakakin sojan Yamen janar Yahya Sari ya yi, ya bayyana cewa; Sun kai harin ne akan cibiyar samar da wutar lantarki

A wata sanarwa da kakakin sojan Yamen janar Yahya Sari ya yi, ya bayyana cewa; Sun kai harin ne akan cibiyar samar da wutar lantarki ta birnin Haifa.

Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa wani makami mai linzami da aka harbo daga Yemen ya sauka akan birnin Haifa,tare da tashin jiniyar gargadi.

Tashar talabijin ta 12 ta HKI ce ta bayar da labarin saukar makami mai linzamin a cikin birnin wanda shi ne na biyu a HKI bayan Tel Aviv. Sai dai majiyar sojan ‘yan sahayoniya ta ce, makamanta sun yi nasarar kakkabo makamin gabanin ya fadi.

A gefe daya  Jiragen yakin Amurka da na Birtaniya sun kai jerin hare-hare akan kasar Yemen sau uku a yankin Sa’adah.

Tashar talabijin din “almasirah’ ta kasar Yemen ta watsa labarin da yake cewa, jiragen yakin na HKI sun kai hare-haren ne dai a yankin Saadah dake arewa maso yammacin kasar.

Wannan harin dai ya zo ne jim kadan bayan da sojojin kasar Yemen su ka kai wa HKI hari ta hanyar harba makami mai linzami da safiyar yau Lahadi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments