Rundunar sojin Yemen ta sanar da nasarar kai hare-hare kan bututun mai na Saudiyya da filin jirgin saman birnin Riyadh
Kakakin Rundunar Sojin Yemen Janar Yahya Sari’e ya bayyana sabbin hare-haren da rundunonin sojin Yemen suka kai wa Saudiyya da sauran sassan da ke da alaƙa da ita.
Kamfanin Dillancin Labaran Mehr ya ambato daga kafar Al-Masirah, cewa Janar Yahya Sari’e, kakakin Rundunar Sojin Yemen ya sanar da cewa: Rundunonin sojin Yemen sun kai hare-haren daukan fansa kan Filin Jirgin Sama na Sarki Khalid da ke birnin Riyadh na Saudiyya da makamai masu linzami.
Ya kara da cewa: “Sun kuma kai hare-hare kan tashoshin famfo mai na bututun mai na gabas da yamma a Saudiyya da jiragen sama marasa matuka ciki da dama.”
Sari’e ya jaddada cewa: “Sun kuma yi nasarar kai hare-haren soji guda biyu a kan wuraren tattarawa da rumbunan makamai na sojojin da Saudiyya ke marawa baya a Aden da Lahj a Yemen. An gudanar da wadannan hare-haren ta hanyar harba makamai masu linzami da dama a yankin Salahuddeen da ke Aden da al-Wahatt a Lahj.”
Ya ce: “Waɗannan makamai masu linzami sun kai hari kan wuraren da aka saita su daidai, inda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama a tsakanin sojojin da Saudiyya ke marawa baya tare da lalata makamansu da rumbunan kayan aikin soja. Badr al-Harbi, wani jami’in Saudiyya, shi ne ke kula da wadannan rumbunan makamai.”