Sojojin Yemen Sun Kai Hare-Hare Kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Ciki Har Da Birnin Tel Aviv

Sojojin Yemen sun kai wani sabon hari da makamai masu linzami kan tsakiyar birnin Tel Aviv fadar mulkin haramtacciyar kasar Isra’ila Kakakin rundunar sojin kasar

Sojojin Yemen sun kai wani sabon hari da makamai masu linzami kan tsakiyar birnin Tel Aviv fadar mulkin haramtacciyar kasar Isra’ila

Kakakin rundunar sojin kasar Yemen Birgediya Janar Yahya Sari’e a safiyar yau Alhamis ya sanar da cewa: Sojojin Yemen sun harba makamai masu linzami kan manyan yankuna da suke tsakiyar haramtacciyar kasar Isra’ila musamman kan birnin Tel Aviv fadar mulkin yahudawan sahayoniyya, kamar yadda kafar yada labaran yahudawan sahayoniyya ta tabbatar da hakan.

Majiyar yada labaran yahudawan sahayoniyya ta rawaito cewa: An yi ta jin karar harbe-harbe a yankuna da dama bayan harba makami mai linzami daga kasar Yemen, yayin da aka ji karar tashin bama-bamai a tsakiyar birnin Tel Aviv fadar mulkin kasar ta Isra’ila.

Haka nan kafafen yada labaran yahudawan sun watsa rahoton cewa: Sama da yahudawan sahayoniyya miliyan guda ne suka garzaya zuwa mafakar karkashin kasa sakamakon fadowar makamai masu linzami a ynakin Gush Dan, tsakiyar haramtacciyar kasar Isra’ila.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments