Sojojin Yemen Sun Harbo Wani Jirgin Yakin Amurka MQ-9 Reaper

Dakarun Yemen sun ce sun yi nasarar harbo wani jirgin Amurka mara matuki kirar MQ-9 Reaper wanda ke gudanar da “ayyukan kiyayya” a tsakiyar lardin

Dakarun Yemen sun ce sun yi nasarar harbo wani jirgin Amurka mara matuki kirar MQ-9 Reaper wanda ke gudanar da “ayyukan kiyayya” a tsakiyar lardin Al-Bayda.  

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar din da ta gabata, rundunar sojin Yemen ta sanar da cewa, dakarun tsaron sama sun yi amfani da makami mai linzami da aka kera wajen kai harin.

Sanarwar ta kara da cewa jirgin MQ-9 Reaper maras matuki shi ne irinsa na 13 da sojojin Yemen suka lalata tun bayan da suka kaddamar da hare-haren goyon bayan Falasdinu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments