Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojin kasar Yamen sun kai hare hare masu karfi kan wasu muhimman wurare a matatar man Aramco na kasar sudiya dake birnin riyad, inda suka yi amfani da makami mai linzami na ballistic da jiragen sama marasa matuki , a matsayin mayar da martani kan hare haren da kasar saudiya take kai wa a birnin sana’a da sauran yankunan kasar
Wadannan hare haren sun zo ne bayan da kasar saudiya ta kai hari a babban birnin kasar yamen da sauran yankuna inda ta harba makamai masu linzami sau 60 a tsawon kwanaki 24 da suka gabata, adadin hare haren da kasar saudiya ta kai kan kasar yamen a baya bayan nan ya kai sau 1410.
Kai hare haren mayar da martani kan muhimman wurare a matatar mai ta Aramco a birnin Riyadh ya nuna irin karfin sojin kasar Yamen akan kasar saudiya, da aka ganin a yan makwannin nan, da kuma harin da kasar saudiya ke kai wa a yankunan fararen hula da muhimman wurare da kuma yankunan dake da cinkoson jamaa