Sojojin Yamen Sun Kai Hari A Kamfanin Mai Na Aramco A Saudiya

Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojin kasar Yamen sun kaddamar da hari da jiragen sama marasa matuki a kan babban kamfanin man fetur da iskar

Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojin kasar Yamen sun kaddamar da hari da jiragen sama marasa matuki a kan babban kamfanin man fetur da iskar gas na Aramco dake  kasar Saudi arebiya a matsayin mayar da martani kan takunkumin da ta sanya wa kasar na tsawon shekaru

Kamfanin dillancin labaran Saba na kasar Yamen yace wata majiyar soji ta bayyana cewa dakarun sojin kasar yamen sun kaddamar da wasu hare-hare soji cikin nasara a yau talata a  kamfanin mai na kasar saudiya wato Aramco, kuma harin yana zuwa ne a matsayin mayar da martani kan harin da saudiya ta kai  a biranan Sa’aada da Hajjah dake arewacin kasar

Dakarun sojin kasar yamen sun sanar da cewa za su ci gabba da kai hare-hare idan aka kai musu hari, kuma za su auna muhimman wurare masu muhimmanci a cikin biranen kasar saudiya da kuma wuraren da aka tattara sojojin gona  a cikin kasar, A Jiya litinin ministan harkokin wajen kasar yamen ya fadi cewa dakarun sojin kasar suna ci gaba da bibiyar irin ci gaban da ake samu, kuma ya jaddada cewa za su mayar da martani mai tsanani kan duk wata barazana da makiya za su yi , don haka dakarun su idonsu a bude yake kuma a shirye suke su sadaukar da rayuwarsu fiye da kowanne lokaci a baya, kuma ba za su ji shayin mayar da martani kan duk wani mataki da saudiya za ta dauka ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted