Sojojin Yamen Sun Harbor Jirgin Yakin Saudiya A Yankin Mokha

dakarun sojin kasar yamen sun kakkabo jirgin yakin kasar Saudia dake kai musu har

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Yamen Bigadier janar Yahya Saree ya sanar cewa da safiyar yau laraba sun yi amfani da wani makami na zamni kuma sun harbo jiragen yakin kasar saudiya dake kai hare hare a kasar yamen

Kafafen yada laban kasashen larabawa sun bada rahoton cewa an ji karar fashewar wani abu mai karan gaske a birnin riyad da safiyar yau laraba, da ake kyautata zaton harin dakarun kasar yamen ne da suka kai da makami mai linzami da kuma jiragen yaki marasa matuki, kuma tuni aka dakatar da duk wasu ayyuka a filin hawa da sauka na birnin Riyad.

Wannan ci gaban yazo ne bayan da kasar saudiya ta kara fadada hare haren soji da take kai wa kan kasar yamen da kokarin durkusar da gwamnatin Sana’a, inda jiragen yakin saudiya suka kaddamar da daruruwan hare hare fadin kasar yamen kamar yadda Saree ya bayyana sun kai hari sau 760 a ranar 20 ga watan satumba.

A ranar 10 ga watan satumba ne dakarun sojin kasar yamen suka kori yan koran saudiya suka kwace muhimmiyar tashar jiragen ruwa ta Mokha , inda suke bude hanyar isa zuwa ga babul mandab, a ranar da ta zagoyo kuma sojojin yamen suka kori yan koran saudiya daga yankuna 6,a taiz da hudaida suka kwace iko da yankin da ya kai fadin kilo mita5400

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted