Kafafen watsa labaran HKI sun ambaci cewa wani makami mai linzami da aka harbo daga kasar Yemen ya sauka akan birnin Haifa, tare da tashin jiniyar gargadi.
Tashar talabijin ta 12 ta HKI ce, ta bayar da labarin saukar makami mai linzamin a cikin birnin, wanda shi ne na biyu a girma a cikin biranen HKI bayan Tel Aviv. Babban birnin kasar.
Amma majiyar sojojin HKI ta ce, makamanta sun yi nasarar kakkabo makamin na kasar Yemen gabanin ya fadi.
Wannan dai ba shi ne karon farko da sojojin Yemen din suke harba makamai masu linzami zuwa HKI ba, don tallafawa Falasdinawa a Gaza, da kuma mayar da martani a kan hare-haren da sojojin HKI su ke kai wa kasar ta Yemen.
Tun bayan da HKI ta shelanta yaki a kan kasar Yemen, a ranar 7 ga watan Octoban shekarar 2023 ne, sojojin Yemen din su ka shiga yaki da HKI don tallafawa Faladinawa, musamman mutanen Gaza da suke fuskantar kisan kiyashi.
Hare-haren na sojojin Yemen dai ya kunshi amfani da makamai masu linzami da kuma jiragen sama marasa matuki.
Tun da fari, sojojin na Yemen sun hana duk wasu jiragen ruwan kasuwanci masu wucewa ta tekun “ Red-Sea” masu zuwa HKI musamman tasahr jiragen ruwa Eliat wacewa da tekun na ‘Red Sea”.
a HKI.
Yemen ta sha sanar da cewa, ba za ta daina kai wa HKI hari ba har sai idan an kawo karshen yakin Yemen da kuma daukewa Gaza takunkumi.