Sojojin Syria Sun Karyata Ficewa  Daga Garin Hums

Rundunar sojan kasar Syria ta karyata labarun da ake watsawa na cewa ta janye daga garin Hums, tana mai tabbatar da cewa tana kai hare-hare

Rundunar sojan kasar Syria ta karyata labarun da ake watsawa na cewa ta janye daga garin Hums, tana mai tabbatar da cewa tana kai hare-hare zuwa garuruwan Darul-Kabirah, Tambisiyyah da kuma al-Rastan dake daura da Hums.

Sanarwar sojojin ta kuma cigaba da cewa adaidai lokacin da suke kai hare-haren ta kasa, su kuma jiragen sama na Syria da Rasha suna kai wasu hare-hare akan masu dauke da makamai.

Majiyar ta kara da cewa masu dauke da makaman sun fada cikin razani sanadiyyar hare-haren na sojojin Syria da Rasha. Wasu daruruwan masu dauke da bindiga  sun halaka yayin da wasu kuma su ka  jikkata. Haka nan kuma an rusa da lalata makamai da motocinsu na yaki.

A  tsakiyar birnin Hums kuwa, majiyar soja ta  ce babu gaskiya akan cewa sun janye daga cikin garin Hums da gefensa.

A jiya jiragen yakin na Syria da Rasha sun kai wasu hare-haren a kusa da garin Talbisiyah wanda ya yi sanadin halakar da dama daga cikinsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments