Sojojin Syria Kun Kori ‘Yan Ta’adda Daga Yankunan Halab Da Idlib

Da safiyar yau Juma’a ne dai  sojojin gwamnatin Syria su ka yi nasarar korar  ‘yan ta’adda da su ka yi kokarin shiga cikin garuruwan Halab

Da safiyar yau Juma’a ne dai  sojojin gwamnatin Syria su ka yi nasarar korar  ‘yan ta’adda da su ka yi kokarin shiga cikin garuruwan Halab da kuma Idlib, bayan da aka yi bata-kashi mai tsanani da su.

A wata sanarwar da ma’aikatar tsaron kasar Syria ta fitar ta bayyana cewa, sojojin kasar sun yi nasarar korar ‘yan ta’adda da su ka  yi kokarin kutsawa cikin garuruwan Halab da kuma Idlib.

Tun a daren Laraba wayewar garin Alhamis ne dai ‘yan ta’addar da kashashen turai suke goyon baya su ka kai gagarumin hari a cikin wadannan muhimman garuruwa na Syria da zummar shimfida iko a cikinsu.

Mayar da martanin da sojojin na Syria su ka yi, ya haddasawa ‘yan ta’addar hasara mai yawa ta rayuka da kuma makamai.

Kungiyar ‘yan ta’adda ta “Hayat Tahrir al-Sham” da sauran kungiyoyin ta’adda da suke kawance da ita sun fara kai harin ne a ranar Larabar da ta wuce.

Sojojin kasa na Syria da kuma taimakon jiragen yaki na Rasha sun kai wa ‘yan ta’addar hari tare da tilasta musu janyewa da baya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments