Sojojin Siriya sun tunkari yankin Al-Safira da ke birnin Aleppo tare da tarwatsa gungun ‘yan ta’adda a hanyar Khanaser.
Dakarun kasar Siriya sun tunkari garin Al-Safira da ke birnin Aleppo, yayin da suka yi nasarar tarwatsa wani gungun kungiyoyin masu dauke da makamai a kan hanyar Khanaser-Athriya, a daidai lokacin da sojojin suke kara zurfafawa a yankunan kudancin birnin Aleppo.
Manazarta harkokin soji sun jaddada cewa: Ci gaban da sojojin Siriyan suke samu na yin kutse a yankin Al-Safira hakan na nufin za su koma cikin sauri cikin yankunan karkarar lardin Aleppo.
Tun da farko, a yammacin jiya litinin, sojojin kasar Siriya sun sanar da cewa: Sun sake kwace iko da kauyukan dake kan hanyar Muhardah al-Suqaylabiyah a cikin karkarar lardin Hama dake tsakiyar kasar ta Siriya.
Kamar yadda, majiyar rundunar sojin Rasha a kasar Siriya ta sanar da cewa an kashe ‘yan ta’adda kusan 100 a cikin sa’o’i 24 da suka gabata a Siriya a hannun sojojin Siriya tare da taimakon sojojin saman Rasha.