Sojojin Siriya sun kashe tare da raunata daruruwan ‘yan ta’adda

Sojojin Siriya sun kashe tare da raunata daruruwan ‘yan ta’adda da ke samun goyon bayan kasashen waje a yayin farmakin ramuwar gayya a arewacin kasar.

Sojojin Siriya sun kashe tare da raunata daruruwan ‘yan ta’adda da ke samun goyon bayan kasashen waje a yayin farmakin ramuwar gayya a arewacin kasar.

“Dakarun mu sun yi nasarar haddasa asara mai yawa a kan kungiyoyin [‘yan ta’adda] da ke kai hare-hare tare da yin sanadin mutuwar daruruwa daga cikinsu,” in ji babban kwamandan rundunar sojin kasar a wata sanarwa.

Sojojin na Siriya sun kuma “lalata motoci masu sulke da dama da kuma wasu motoci kuma sun sami damar harbo tare da lalata jirage marasa matuka guda 17,” in ji ta.

A halin da ake ciki dai sojojin sun yi nasarar sake kwace wasu yankuna a cikin sa’o’i da suka gabata, sanarwar ta ce sojojin za su ci gaba da yakin da suke yi har sai an samu nasarar fatattakar ‘yan ta’addar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments