Ma’aikatar tsaron kasar Siriya ta bada sanarwan samun cikekken iko a kan tashar jiragin sama na Tabaqah ta sojoji da ke wajen birnin Riqqah a arewacin kasar Siriya.
Tashar talabijin ta Al-Mayaddeen ta kasar Lebanon ta nakalto majiyar kungiyar kurdawa ta ‘Kasad’ tana cewa sun fafata da sojin Damask a wajen birnin Riqqah.
Gwamnatin Siriya ta kara da cewa ta kwace iko da wadan nan yankuna a hannun kungiyar ‘raya democradiyya ta Siriya wato ‘Kasad’ sun kuma kace wasu wurare daga hannunsu, amma sun gano cewa mayakan Kasad sun kashe fursinoni da fursinonin yaki da dama a garin Tabaqah kafin su fice daga yankin.
Kimani wata guda kenen sojojin gwamnatin Siriya da kuma na kungiyar kurdawa mai neman bellewa daga kasar Siriya suka yi ta fafatawa a tsakaninsu don tabbatar da ikonsu a arewacin kasar ta Siriya.
Banda haka sojojin Julani sun ce sun kama mutane 30 a garin Tabaqah wadanda suke kokarin tada hankali, sun kuma kaisu inda ya dace da su.