Manufar rawar dajin ta sojojin ruwan kasashen biyu ta kunshi hanyoyin tabbatar da tsaro a doron ruwa, da kuma ayyukan ceto da agaji. Jiragen ruwan Iran da su ka shiga cikin wannan atisayen sun hada da “Jamran” da kuma babban jirgin ruwa mai harba makamai masu linzami.
Kasashen Iran da Oman makwabtan juna ne da suke da iyakoki na ruwa.