Babban kwamandan sojojin ruwa na JMI ya bada sanarwan cewa sojojinsa sun fara atisaiy daga farkon takun farisa har zuwa bakin mashigar ruwa ta Hurmus.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Alireza Tangsiri babban kwamandan sojojin ruwa na rundunar IRGC yana fadar haka a yau jumma’a. Ya kuma kara da cewa a shekarum baya rundunar sa ta sha yin atisayen hadin guiwa tare da wasu kasashen yankin da kuma wasu daga nesa a yankin don tabbatar da tsaron yankin don kuma musayar fasahar yaki tsakanin kasashen.
Tangsiri ya kara da cewa a wannan karon dan kadanne daga sojojin ruwa na rundunar IRGC ne suke gudanar da wannan atisayen.
Sannan ya bayyana manufar wannan atisayen a matsayin ta abota da zaman lafiya ga kasashe makobta sannan gargadi ga makiyan JMI.
Kwamandan ya kara da cewa rundunar a wannan atisayen zasu kaddamarda sabbin jiragen ruwa masu saurin da kuma makamai masu linzami daga gaba zuwa cikin teku.
Sojojin ruwa na rundunar IRGC zasu nuna korewansu a wannan atisayen inji shi.