Rundunar Sojin Najeriya, ta musanta jita-jitar da ake yadawa cewar an kafa sansanin sojojin Faransa a Maiduguri, Babban Birnin Jihar Borno.
A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Kaftin Reuben Kovangiya, ya fitar.
Ya bayyana cewa babu gaskiya a zancen, kuma bidiyon da ake yadawa ba shi da alaka da sojojin Faransa.
Kaftin Kovangiya, ya yi karin haske cewa jami’in da aka gani a bidiyon ba sojan Faransa ba ne.
Ya ce mamba ne na kungiyar bayar da shawara kan harkokin soji ta Birtaniya (BMATT), wadda ke aiki tare da sojojin Najeriya wajen yaki da ‘yan ta’adda.
Ya yi gargadi kan yada jita-jita da labaran karya a shafukan sada zumunta.
Sojojin Najeriya sun jaddada cewa suna ci gaba da hada kai da abokan huldarsu na kasa da kasa domin magance matsalolin tsaro da ke addabar kasar.