Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Kai Samame Al-Quneitra Na Siriya

Sojojin mamayar Isra’ila sun mamaye al-Quneitra a Siriya kuma sun kai hari kan gidajen Jama’a Tashar labarai ta Al-Ikhbariya Al-Suriya ta ruwaito cewa: Sojojin mamayar

Sojojin mamayar Isra’ila sun mamaye al-Quneitra a Siriya kuma sun kai hari kan gidajen Jama’a

Tashar labarai ta Al-Ikhbariya Al-Suriya ta ruwaito cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun shiga ƙauyen al-Rafid da ke Al Quneitra, kudancin Siriya, a daren Lahadi, kuma suka gudanar da bincike kan gidajen jama’a da dama.

Tashar ba ta bayar da ƙarin bayani game da girman rundunar da suka kai farmakin ba, ko kuma labarin kama mutane ba kamar yadda labarin ko sojojin na Isra’ila sun janye daga garin ba.

Wannan mamayar ta zo ne a daidai lokacin da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ke ci gaba da keta haƙƙin mallakar Siriya.

Kuma kafin nan Shugaban kasar Siriya Ahmed al-Shar’a ya yi Allah wadai da ci gaba da keta haƙƙin Siriya da ke lalata tsaron yankin baki ɗaya, ya yi kira ga Isra’ila da ta janye daga yankunan da ta mamaye a kudancin Siriya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted