Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Hare-Haren Wuce Gona Da Iri Kan Gaza

Falasdinawa biyu ne suka yi shahada yayin da wasu da dama suka samu raunuka sakamakon hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamayar Isra’ila suka

Falasdinawa biyu ne suka yi shahada yayin da wasu da dama suka samu raunuka sakamakon hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan Zirin Gaza

Bafalasdine guda ne ya yi shahada kuma wasu tara na daban suka samu raunuka – a jiya Asabar – sakamakon jerin keta yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra’ila ta yi a yankin Gaza.

Majiyar lafiya a Asibitin al-Awda ta ruwaito cewa: Wani matashin bafalasdine ya yi shahada sakamakon harbinsa da bindiga da sojojin mamayar Isra’ila suka yi a arewa maso gabashin sansanin al-Nusirat a tsakiyar Zirin Gaza.

A birnin Deir al-Balah, Majiyar lafiya a Asibitin Shahidai na Al-Aqsa ta ruwaito cewa: Falasdinawa 3 ne suka samu raunuka kuma daya daga cikinsu rauninsa ya munana sakamakon harin da jirgin sama maras matuki ciki ya kai kan babur a kan titin Salahudden.

Wata majiya ta yankin ta tabbatar da cewa: Wasu Falasdinawa biyu sun ji raunuka sakamakon harbi da manyan bindigogi da sojojin mamayar Isra’ila suka yi a yankunan Khan Yunis, yayin da na uku ya ji rauni a hannun sojojin mamayar Isra’ila a yankin Al-Mawasi. Mutane biyu sun ji rauni a birnin Gaza sakamakon bude wutar bindiga kan dudun gabashin unguwar al-Zaytoun, baya ga

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted