Sojojin Mali Sun Sake Kwace iko Da Kidan Bayan Ficewar Yan Tawaye

sojojin kasar mali sun kara samun nasara wajen kwace ikon kula da yankin kidan bayan korar yan tawaye

Sojojin Mali sun sake kwace iko da Kidal, birnin da ke da muhimmancin gaske a yankin arewacin kasar, wanda akalla ya shafe watanni biyar a karkashin ikon ‘yan tawayen Abzinawa, wadanda suka janye daga cikin birnin a jiya Talata.

Wani jami’in soja a birnin Gao, da ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce a halin yanzu sojojin na Mali sun tsaurara matakai gami da aikin sintiri a birnin na Kidal da kewayensa da zummar kakkabe duk wata barazanar tsaro.

Sai dai kungiyar FLA ta mayakan Abzinawan ta ce  janyewar da ta yi ta wucin gadi ce, haka zalika ta dauki matakin ne domin kare rayukan fararen hula daga salwanta, la’akari  da barin wuta ta sama na mai kan uwa da wabi da ta ce haɗin gwiwar sojojin na Mali da na Rasha na yi kan garin na Kidal.

A karshen watan Afrilun wannan shekara ne dai, mayaƙan Abzinawan na FLA suka kaddamar da jerin-hare-hare da nufin raunana gwamnatin sojin Mali, lamarin da ya kai ga kwace iko da birnin Kidal da kuma kashe ministan tsaron kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted