Babban hafsan sojojin kasar Iran ya bayyana goyon bayan sojojin kasar Iran ga kasar Qatar, bayan hare-haren da HKI ta kai kan birnin Doha na kasar a ranar laraba a kokarinta na kashe shuwagabannin kungiyar hamas na kasar Falasdinu da ta mamaye.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Brigadier General Mousavi yana fadar haka a yau, ya kuma bayyana cewa wannan matakin ya zo dai-dai da akidar kasar na tallafawa duk wanda yake gaba da HKI a yankin ko a wani wuri.
Janar Musavi ya kara da cewa, muna son shaidawa gwamnatin kasar Qatar kan cewa, sojoji da gwamnatin JMI suna tare da ita har zuwa karshe.
Musavi ya ce: Kowa ya sani, kamar yadda shugaba Pezeshkiyan ya fada, wannan Haramtacciyar kasar ba za yi abinda take yi ba, in ba don tallafi da goyon bayan kasashen yamma ba.
Ministan tsaron kasar Qatar a zantawarsa ta wayar tarho da shugaba Pezeshkiyan bayan harin, ya godewa JMI da mutanen kasar kan irin goyon bayan da suke bawa kasarsa.