Sojojin Isra’ila Sun Sabawa Yerjejeniyar Tsagaita Wuta Da Aka Cimma

Sojojin kasar Labanon sun zargi Isra’ila da ta kai wani hari ta sama kan wata cibiyar Hizbullah da ke kudancin kasar ta Lebanon, da saba

Sojojin kasar Labanon sun zargi Isra’ila da ta kai wani hari ta sama kan wata cibiyar Hizbullah da ke kudancin kasar ta Lebanon, da saba yarjejeniyar tsagaita bude wuta” da ta fara aiki a jiya.

Tsagaita bude wuta tsakanin Isra’ila da kungiyar Hizbullah ta fara aiki da sanyin safiyar Laraba a kasar Labanon, bayan shafe sama da shekara guda ana gwabza fada a kan iyakokin kasar da watanni biyu ana gwabza fada tsakanin sojojin Isra’ila da kuma kungiyar gwagwarmaya ta Lebanon.

Tunda farko dai Shugaba Joe Biden na Amurka ya ce yarjejeniyar dakatar da bude wutar wadda kasarsa da Faransa suka jagoranta ta nuna cewa za a iya cimma zaman lafiya.

A nasa bangare kuwa sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana cewa, rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Lebanon UNIFIL za ta taimaka wajen aiwatar da yarjejeniyar.

Masar da Jordan sun bayyana fatan yarjejeniyar za ta kai ga gagarumin kuduri na cimma dakatar da bude wuta a Gaza.

Firaministan Labanon Najib Mikati ya yi maraba da yarjejeniyar, yana mai cewa wani muhimmin mataki ne na maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar tare da bai wa ƴan kasar damar komawa gida.

Iran kuwa ta bakin Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ya jaddada goyon bayan Iran ga gwamnatin Lebanon da al’ummarta da kuma ‘yan gwagwarmaya, yana mai cewa Tehran ta dade tana jaddada bukatar dakatar da kai farmakin da Isra’ila ke kai wa Gaza da Lebanon cikin gaggawa. Watanni 14 kafin wannan burin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments