Sojojin mamayar Isra’ila sun kai hare-hare kan ‘yan kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas da na Jihadul- Islami a Gaza
Rundunar sojin mamayar Isra’ila ta sanar da cewa, tare da hadin gwiwar Hukumar Tsaron Isra’ila (Shin Bet), ta kai hare-hare ta sama kan Zirin Gaza a ranar Asabar da kuma a cikin ‘yan kwanakin nan, wanda ta ce ya yi sanadiyyar mutuwar wasu shugabannin kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa daga Hamas da Jihadul- Islami.
Kakakin rundunar sojin mamayar Isra’ila Ella Wawiya ta bayyana a shafinta na Facebook cewa: Rundunar ta kai hari kan wasu mutane da ta kira “manyan jami’ai” a lokacin wani taro da ta kira a birnin Gaza a safiyar Asabar.
A wani hari ta sama da aka kai a yau a unguwannin Daraj da Tuffah da ke arewacin birnin Gaza, rundunar sojin ta ce ta kashe Muhammad Walid al-Nakhalah, tana mai bayyana shi a matsayin kwamandan tsarin makami mai linzami na reshen soja na kungiyar Jihadul-Islami.
Sanarwar sojojin mamayar ta Isra’ila ta kuma ce ta kai hari ta sama a ranar Laraba da ta gabata a yankin Khan Younis da ke kudancin Gaza, inda ta kai harin kan Muhammad Abu Shalouf, wanda ta bayyana a matsayin kwamandan kamfani a reshen soja na kungiyar Jihadul-Islami, tana mai ikirarin cewa yana da hannu a harin da aka kai a ranar 7 ga Watan Oktoban shekara ta 2023.