Sojojin “Isra’ila” Sun Kai Hare-hare A Kudancin Lebabon

Sojojin mamayar Haramtacciyar Kasar Isra’ila sun kai wasu hare-hare a garuruwan “Ayna-Qana da Kafar Tabniyata da suke a kudancin Lebanon a arewa da tafkin Laitani,

Sojojin mamayar Haramtacciyar Kasar Isra’ila sun kai wasu hare-hare a garuruwan “Ayna-Qana da Kafar Tabniyata da suke a kudancin Lebanon a arewa da tafkin Laitani, a kusa da Nabdhiyyah.

Tashar talabijin din ‘almayadin’ mai watsa shirinta daga kasar Lebanon ta bayar da labarin dake cewa; ‘yan sahayoniyar sun kai harin ne dai ta sama akan wasu gidaje biyu a cikin wadannan garuruwan,bayan a baya su ka yi barazanar cewa za su kai harin.

Tun da fari wani jirgin sama maras matuki na ‘yan sahayoniyar ya kai wani hari akan wata mota a garin “Qalilah” dake gundumar  Sur a kudancin Lebanon. A sanadiyyar hakan mutum daya ya yi shahada, yayin da wasu 8 su ka jikkata.

Bugu da kari, wani jirgin sama maras matuki na sojojin na mamaya ya jefa bama-bama guda 3 a garin Aytas-sh’ab a kudancin Lebanon. Dama tun da safiyar jiya Litinin din ne dai sojojin mamayar su ka kai wa garin wasu jerin hare-hare.

Wadannan hare-haren dai suna a karkashin keta yarjejeniyar tsagaita wutar yaki da aka cimmawa a tsakanin Lebanon da Haramtacciyar Kasar Isra’ila  a ranar 26 ga watan  Nuwamba 2024, da kuma kudurin MDD mai lamba 1701 da aka fitar da shi a 11 ga watan Ogusta na 2006.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted