Isra’ila na ci gaba kai Hare-hare Kan Gaza

Isra’ila ta ƙaddamar da sabbin hare-hare ta sama da manyan bindigogi a Gaza, wanda ke nuna yadda take ci gaba da karya yarjejeniyar tsagaita wuta

Isra’ila ta ƙaddamar da sabbin hare-hare ta sama da manyan bindigogi a Gaza, wanda ke nuna yadda take ci gaba da karya yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma toshe hanyoyin agajin jin kai da yankin Falasdinawa ke matukar bukata.

Kafafen yada labarai na Falasdinawa sun ruwaito cewa Isra’ila ta yi ruwan bama-bamai a gefen gabashin birnin Gaza a safiyar Alhamis.

Jiragen saman yaki na Isra’ila sun yi ruwan bama-bamai a yankunan gabashin Rafah, da ke kan iyakar kudancin Gaza da Masar.

Mazauna yankin sun kuma bayar da rahoton wani hari ta sama a gabashin birnin Deir al-Balah a tsakiyar yankin Gaza.

Babau karin bayyani kan irin ta’asar da aka samu ta hasarar rai ko barna zuwa lokacin farasa wadanan labaran.

Bugu da kari, sojojin Isra’ila sun bude wuta a unguwannin Gaza da Khan Younis, inda aka rushe gine-gine.

Ƙungiyar gwagwarmayar Hamas ta musanta duk wani hannu a fashewar da ta faru a Rafah, a kudancin yankin Gaza, wanda ya haifar da kwantar da wani jami’in Isra’ila a asibiti.

Kungiyar ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa fashewar ta faru ne a yankin da sojojin Isra’ila ke iko da shi gaba daya inda babu Falasdinawa a wurin, kuma ta yi gargadin cewa akwai ababe masu fashewa a yankin da kuma wasu wurare.

Ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza ya bayyana cewa sojojin Isra’ila sun karya yarjejeniyar tsagaita wuta sau 875 tun lokacin da ta fara aiki a ranar 10 ga Oktoba.

Tun daga watan Oktoba na 2023, sojojin Isra’ila sun kashe Falasdinawa akalla 70,937, galibi mata da yara, tare da raunata 171,192 a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted