Kafofin yada labaran Isra’ila sun ce akalla sojojin kasar 825 ne aka kashe a zirin Gaza tun a watan Oktoban da ya gabata.
Kafofin yada labaran yahudawan sun kuma ce an kashe sojojin Isra’ila akalla 40 a birnin Jabalia da ke arewacin Gaza tun a watan da ya gabata, inda gwamnatin kasar ta tsananta hare-haren da take kai wa birnin.
A halin da ake ciki rahotanni sun ce an kashe sojojin Isra’ila akalla guda daya tare da jikkata wasu da dama bayan da mayakan Falasdinawa suka far wa sojojin a birnin Beit Hanoun da ke arewa maso gabashin birnin Gaza.
Wannan lamari dai na zuwa ne a daidai lokacin da yakin ya yi sanadin shahadar Falasdinawa kusan 45,550, galibinsu mata da kananan yara.