Sojojin Iran 7 Sun Yi Shahada A Hare-haren Amurka A Kudancin Kasar

Majiyar sojojin Iran ta tabbatar da shahadar sojojin 7 a wasu hare haren da jiragen yakin Amurka suka kai kan barikin sojoji na Bampur a

Majiyar sojojin Iran ta tabbatar da shahadar sojojin 7 a wasu hare haren da jiragen yakin Amurka suka kai kan barikin sojoji na Bampur a lardin Sistan Baluchistan na kudancin kasar a daren jiya.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto majiyar sojojin JMI na bada sanarwan shahadar sojojinta har guda 7 a hare haren makiya kan barikin sojoji da ake kira Bampur a garin Iranshahr na yankin S/B., kuma tuni sun maida martani kan sojojin Amurka a yankin.

Majiyar ta ce makaman Amurka sun fada a kan wuraren kwana na sojojin kasar da kuma na zamansu a cikin barikin a safiyar Laraba inda suka cilla makamai masu linzami har guda 13 a kansu.

Labarin ya kara da cewa sojojin 7 sun yi shahada a nan take, sannan wasu da dama sun jinya a asbitocin yankin.

Daga karshe majiyar ta kammala da cewa tuni an fara maida martani kan sojojin Amurka a yankin sannan za’a ci gaba da hakan na wani lokaci.

A lardin Ahwaz na kudu maso yammacin kasar kuma mutanen yankin sun bada labarin jin karar fashewa a wasu wurare daga ciki har da wani wuri kusa da asbitin jinyar yara kanana masu fama da cutar daji ko kansa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted