Sojojin HKI Suna Cigaba Da Kutsawa Cikin Syria

A yau Alhamis sojojin mamayar HKI sun cigaba da kutsawa cikin yankunan kasar Syria da su ka hada da babbar madatsar ruwan kasar a yankin

A yau Alhamis sojojin mamayar HKI sun cigaba da kutsawa cikin yankunan kasar Syria da su ka hada da babbar madatsar ruwan kasar a yankin kunaidara.

Wannan yana nuni da cewa ya zuwa yanzu sojojin mamayar HKI sun shimfida ikonsu a cikin  cibiyoyin ruwa guda 6 mafi muhimmanci a cikin kasar ta Syria, baya ga mamaye wasu yankunan da suke kusa da babban birnin kasar Damascus.

Madatsar ruwan da sojojin mamayar su ka isa wurinta a bayan nan ita ce ta “ Mandara”.

Tashar talabijin din ‘almayaadin’ ta fadi cewa; wata madatsar ruwan da HKI ta mamaye ita ce ta “alwahda’ da take kan iyaka da Jordan, wanda hakan baraza ce ga Jordan din, bayan Syria.

A gefe daya, kafafen watsa labarun Syria sun bayar da labarin cewa an ji fashewar wasu abubuwa masu karar gaske a yankunan da suke bayan birnin Damascus, wanda daga baya ta bayyana cewa Isra’ila ce  ta kai hari akan tuddan “Shaham” wanda  cibiyar sojan Syria ne.

Wannan cibiyar tana daga cikin cibiyoyin sanarwa mafi muhimmanci na sojan Syria da kuma na’urorin  hango abokan gaba daga nesa, da makamai masu sulke da masu linzami.

Tun bayan kifar da gwamnatin Basshar Asad ne dai HKI take kai wa Syria hare-hare da kuma yin kutse a cikinta tana kame wuraren masu muhimmanci na soja. Sojojin mamayar sun sanar da cewa, sun lalata kaso 80% na makaman kasar Syria.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments