Rahotannin da suke fitowa daga Gaza sun ambaci cewa hare-haren na sojojin mamaya sun yi sanadiyyar shahadar Falasdinawa 31 da kuma jikkata wasu 79.
Ma’aikatar kiwon lafiyar Falasdinu ta ambaci cewa; Sojojin na mamaya sun kai hari akan wasu duro-duro masu dauke da abubuwa masu fashewa a kusa da asibitin “ Kamal-Adwan” dake garin “Beit-Lahiya” a arewacin Gaza.
Ita kuwa hukumar abinci ta duniya (WFP) ta sanar da cewa rashin samun izini daga Isra’ila domin shigar da abinci zuwa Gaza, ya sa mutane miliyan 2 suna fama da karancin abinci.
Har ila yau hukumar abincin ta yi kira da a samar da wata hanya ta kai abinci da kayan bukatar yau da kullum zuwa zirin Gaza domin kawo karshen yunwar da ake fama da ita.
A wasu rahotanni da tashar talbijin din Aljazira ta watsa ta ambaci cewa, da akwai gawawwaki masu yawa a kasa a Gaza da babu halin rufe su, don haka karkuna suke cin namansu.
A wasu wurarenmu an nuna yadda gawawwakin su ka zagwanye ta yadda sun zama kwarangal.
Ya zuwa yanzu adadin wadanda aka iya tantance cewa sun yi shahada sun kai 45,000, yayin da wasu dubbai suke karkashin baraguzai ba a iya isa gare su su.
Mafi yawancin wadanda su ka yi shahada mata ne da kananan yara.