Sojojin HKI Sun Shiga Cikin Yankin Qunaidhara Na Kasar Syria

Tashar talabijin din ‘aljazira’ ta bayar da labarin da yake cewa, sojojin na HKI sun yi kutse cikin yankin Qunaidhara da motoci 10 da safiyar

Tashar talabijin din ‘aljazira’ ta bayar da labarin da yake cewa, sojojin na HKI sun yi kutse cikin yankin Qunaidhara da motoci 10 da safiyar yau Lahadi.

Majiyar ta kara da cewa; sojojin na HKI sun shiga cikin kauyen al-Hanut dake yankin na Qunaidhara a kudancin kasar ta Syria tare da kafa shinge a tsakanin wannan kauyen da kuma Saidah a Julan. Bugu da kari sojojin na HKI sun rika binciken motocin mutanen Syria da suke wucewa ta wannan yankin, tare da yi wa wasu samari da dama tambayoyi.

 Tun bayan kifar da gwamnatin Basshar Asad  Sojojin HKI suke yin kutse a cikin kasar Syria a duk lokacin da su ka ga dama, bayan da su ka rushe kaso 80% na makaman kasar na kasa da sama.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted