Sojojin HKI Sun Kai Hare-hare A Sassa Mabanbanta Na Kasar Yemen

Tashar talabijin din HKI ta channel: 12 ta nakalato sojoji suna sanar da kai wa Yemen hare-hare. Sanarwar ta kuma ce; jiragen yakin HKI sun

Tashar talabijin din HKI ta channel: 12 ta nakalato sojoji suna sanar da kai wa Yemen hare-hare.

Sanarwar ta kuma ce; jiragen yakin HKI sun kai hare-hare ne a wurare 9 a lokuta daban-daban da su ka hada da tashar jiragen ruwa ta Hudaidah.

Sojojin na HKI sun ce jirage 30 ne su ka kai harin. Haka nan kuma sun ce an kai hare-haren ne sau takwas ba a lokaci daya ba.

Daga cikin wuraren da aka kai wa harin har da kamfanin siminti.

Harin na HKI akan Yemen ya zo ne bayan da sojojin Yemen su ka kai wa filin saukar jiragen saman Ben Gorion na HKI hari da makami mai linzami wanda ya dakatar da zirga-zrigar jiragen sama na kasa da kasa.

Kakakin sojan Yemen Janar Yahya Sari, ya fada a jiya Lahadi cewa; Daga yanzu sun kakaba wa HKI takunkumi ta sama, tare da yin kira ga kamfanonin jiragen sama na kasa a kasa da su daina zuwa HKI.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments